Nijar za ta aika soji domin yaki da Boko Haram

Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar kasashen da ke makwaftaka da Nigeria.

A Jamhuriyar Nijar, 'yan majalisar dokokin kasar sun amince gwamnatin kasar ta tura dakarunsu domin yaki da kungiyar Boko Haram da ke Nigeria.

Wannan mataki na zuwa ne bayan mayakan Boko Haram sun kai hari a kan wani gidan yari, da kuma dana bam a wata mota a garin Diffa da ke kudancin kasar.

Ministan tsaro a Nijar, Alhaji Mahamadou Karidjo ya shaida wa BBC cewa kasarsa za ta aike da bataliya guda ta soji zuwa kewayen tafkin Chadi, da cikin kasar Kamaru da Nigeria da kuma kasar Chadi.

A makon jiya ne Boko haram ta kaddamar da hari na farko mafi muni a Jamhuriyar Nijar.

Makwaftan Nigeria dai na ci gaba da fuskantar hare-haren masu tasa kayar bayan a daidai lokacin da 'yan gudun hijira ke tsallaka iyakar kasar domin tserewa hare-haren 'yan Boko Haram da ke ikirarin kafa daular musulunci a kasashen Nigeria, da Chadi da Kamaru da Nijar.