A daina hada Siyasa da Addini

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Ana zargin 'yan siyasar Nigeria da yin amfani da addini a cikin harkokinsu.

Wasu shugabannin Kiristoci daga arewacin Najeriya sun fara ganawa da 'yan siyasa da shugabannin addini a fadin kasar.

Ganawar dai wani mataki ne na nunawa shugabannin matsalar dake tattare da hada addini da siyasa a lokaci guda, lamarin da suka yi zargin na dagula makomar Najeriya a siyasance.

Tuni wasu shugabannin siyasa su ka gargadi Najeriya da ta dauki darasi daga rikicin musulmi da Kiristoci a Sudan.

Wasu daga cikin shugabannin na ganin cewar ana hada siyasa da addini domin cimma wata manufa, dalilin da ya sa ake ta kashe-kashen rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba da hasarar dukiyar da ba a san adadin ta ba.