Talbijin mai sauraron hirar mutane

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin lataroni na Samsung ya yi gargadin cewa mutane su daina hira a kan batutuwan da suka shafi rayuwarsu a gaban talbijin dinsa na komai da ruwanka.

Samsung ya ce talbijin din na sauraron duk wata hira ko magana da aka yi a gaban talbijin din mai amfani da murya wajen daukar umarni.

Haka kuma a cewar kamfanin akwai yiwuwar talbijin din ya aika hirar ko maganar ga Samsung ko kuma wasu daban.

Gargadin dai na kunshe ne a manufofin kamfanin na yin amfani da talbijin din ta hanyar hada shi da hanyar sadarwa ta intanet.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Manufofin dai sun yi bayanin cewa talbijin din zai dinga sauraron mutanen da ke dakin da aka ajiye shi domin jin ko za a bashi umarni.

An dai yi ta baza manufofin kamfanin wanda a baya mutane ba su san da shi ba, a shafin Twitter, abin da ya sa dole sai da Samsung ya fito ya yi karin haske kan yadda talbijin din ke karbar umarni.

Wannan lamari ba kamfanin Samsung kawai ya shafa ba, domin wani kwararre a kan fasahar bayanai a Burtaniya ya gano cewa talbijin dinsa na LG na tattara bayanai kan halayyarsa ta yin kallo.

Yayata wannan batu ne ya tilasta kamfanin LG ya inganta manhajarsa ta yadda ya bai wa mutum damar kashe ta idan baya so wani ya samu bayanansa.