Za a biya diyya ga iyayen da aka yi musayar 'ya'yansu

Image caption Iyayen sun nuna shakku ne saboda launin fatar jikin jariran da kuma tsawon gashinsu a lokacin da aka yi musayar

A Faransa, iyalai biyu da aka yi musu musayar jarirai shekaru 20 da suka wuce za su karbi diyya na fiye da dala miliyan biyu.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke cewa asibitin da lamarin ya faru da ke Cannes ya biya diyyar ga jariran mata da a yanzu sun girma da iyayensu da kuma 'yan uwansu.

A lokacin da aka yi musayar dai iyayensu mata sun nuna shakku game da jariran da aka basu bayan an sanya su a kwalba guda lokacin da aka yi musu maganin cutar shawara.

Iyayen biyu sun hadu shekaru goma da suka gabata a lokacin da aka gano cewa an yi musayar, amma ba su nemi kowacce ta karbi nata 'yar ba.

Daya daga cikin iyaye matan ta ce kasancewa tare da 'yarta ta gaskiya zai yi matukar tayar mata da hankali.