Budurci a Iran: Shawo kan matsalar addini da al'ada

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saurayi da budurwa a wajen shakatawa a Isfahan na Iran.

Budurcin 'ya mace a Iran na da matukar muhimmanci ta fuskar zamantakewa da kuma al'ada.

Hakan ya sa wasu 'yan matan kan je a yi musu tiyata domin maido musu da budurcinsu kafin ranar aure.

Saurayi da budurwa a wajen shakatawa a Isfahan na Iran.

"An kwantar da ni a asibiti. Na yi mummanan hadari, kuma na ji rauni a kwankwaso na. Ina matukar jin radadin ciwo. Sai mahaifiya ta ta bukaci likita ya duba budurci na."

Mahnaza 'yar shekaru 21 ke bayyana haka lokacin da ta yi hadarin mota a arewacin Iran. Wanta da surikarta sun rasu a hadarin. A wajen hukumomi a Iran, ta rasa budurcinta.

Ta ce "A ranar da mahaifiya ta ta ce a gwada budurci na, wani kwararre ya gudanar da gwaje-gwaje, kuma daga karshe ya ba mu wata wasika inda a ciki aka rubuta cewa na rasa budurci na sakamakon hadarin mota."

Muhimmancin Budurci

Budurci a Iran na da matukar muhimanci ta fuskoki da dama duk da wasu sauye-sauyen al'amura a kasar. Bisa la'akari da bukatun addini da al'ada, iyalai da dama na son ganin mace ta kasance da budurcinta kafin ranar aure.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Addini na cikin tsarin rayuwa a kasar Iran

A Jamhuriyar Islama ta Iran, an haramta jima'i kafin aure kuma wanda ya aikata hakan, zai iya fuskantar hukunci a kotu.

Jagoran addini a Iran, Ali Khameni, ya sha nanata bukatar bin tafarkin addini kuma ya ce 'akwai martaba a kan batun budurcin mace."

Budurci ba wai batun addini ba ne kawai a Iran, batu ne na al'ada. Uba ne kadai zai iya aurar da 'yarsa budurwa.

Gwaje-gwaje

Kafin a dauki mace a matsayin budurwa a Iran sai an gwada ta an tabbatar da budurcinta.

Babu alkaluma a hukumance da za su iya tabbatar da adadin wadanda ake gwada budurcinsu a kasar, amma batun na da tayar da hankali ga masu rajin kare hakkin mata.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maaurata a Iran a lokacin biki

An haramta gwada budurci a wasu kasashe, amma babu wata doka a kan haka a Iran. Kotuna a Iran za su iya bayar da umarnin gudanar da gwajin budurci idan aka yi wa mace fyade ko kuma idan mijinta ya yi korafin cewar matarsa ba budurwa ba ce a ranar da ya soma shiga dakinta.

A wasu lokutan iyalan matar za su nemi a yi gwajin budurcin 'yarsu.

Budurwa

Sima 'yar Iran ce wacce aka yi wa gwajin budurci kafin aurenta. Ta ce "Ban yi niyyar yi ba.Iyaye na ne suka matsa min. Mahifiyata kullum sai kuka take yi, mahifina kuma yana fushi da ni. Shi ya sa na yi. Sai aka ce ni budurwa ce."

Amma wasu Iraniyawan na yin jima'i kafin ranar aurensu kuma idan sun samu miji sai su je likita ya yi musu tiyata domin maido musu da budurcinsu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu hijabi a Iran na shiga cikin zanga-zanga

Hymenoplasty ne sunan tiyatar da ke yi wa mata cikin mintuna 30 sa'oi budurcinsu ya dawo.

Dr Elmi, wani likitan mata a Tehran ya ce, "Muna gane wa idan mace ta je an yi mata tiyata domin maido mata budurcinta".

Sanaz ta ce an yi mata tiyatar shekaru uku da suka wuce.

Ta ce "Iyaye na suna bin addini sau da kafa. Ina kwanciya da saurayina amma saboda ba mu yi aure ba, sai muka je likita ya maido mini da budurci na. Sai na samu wani mutumin na aura bayan shekara daya."

*An sauya sunayen mutanen cikin wannan rahoton.