Boko Haram: An hana hawa babura a Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta kai hari a Jamhuriyar Nijar ranar Jumma'a

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin jihar Difa sun hana tuka babura sakamakon rashin tsaron da ake fama da shi.

Hukumomin suna zargin cewa ana amfani da babura domin kai hare haren da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a garin na Difa.

Da ma dai hukumomin sun sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kowacce rana.

Kasar ta Nijar dai tana fama da barazanar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

A ranar Juma'a ta makon jiya ne 'yan kungiyar suka kai hari a karon farko a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

A ranar Litinin ne majalisar dokokin kasar ta amince gwamnati ta tura dakaru a cikin rundunar hadaka ta kasashe mambobin kungiyar tafkin Cadi domin yaki da Boko Haram.