Harin Boko Haram na korar mutanen Diffa

'Yan Boko Haram a Diffa
Image caption 'Yan Boko Haram a Diffa

A jamhuriyar Nijar mazauna yankunan Diffa sun fara gudun hijira zuwa jahar Damagaram mai makwabtaka da Diffa.

Daruruwan mazauna birnin ne a kulli-yaumin ke cika motoci suna ficewa daga garin.

Cikin makon da ya gabata ne 'yan kungiyar Boko Haram suka fara kai hare-hare a wannan yanki.

Sojojin kasar ta Nijer sun sha murkushe yunkurin kai hari na 'yan kungiyar ta Boko Haram, bayan kashe wasu daga cikinsu, ta kuma kame wasu maharan.

Akwai daruruwan dubban 'yan gudun hijira daga Nijeriya da suka nemi mafaka a garin na Diffa sakamakon hare-haren na Kungiyar Boko Haram.

Karin bayani