'Ban gaya wa kowa cewa zan cire Jega ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jonathan na shan suka kan batun dage zabe

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya ce hukumar zaben kasar ba ta sanar da shi ba kafin ta jinkirta ranar zaben kasar ba.

A hirarsa da wasu zababbun 'yan jaridar a fadarsa da ke Abuja, Mr Jonathan ya ce bai da bukatar hukumar INEC ta tuntube shi kafin ta dage ranar zabe domin tana cin gashin kanta ne.

A kan batun shugaban INEC, Furofesa Attahiru Jega kuwa, Mr Jonathan cewa ya yi "Babu wanda na gayawa cewa zan cire Jega."

Tun bayan da aka dage zaben kasar, mutane da dama ke zargin cewa shugaban kasa na da hannu a kan batun.

Ya kara da cewar " Wasu 'yan siyasa na daukar nauyin matasa domin su tayar da hankali."

Mr Jonathan ya ce yana kokarin tabbatar da tsaron kasar saboda aikinsa ne yin hakan.

"Ina son in tabbatar da tsaron al'umma saboda hakan na daga cikin ginshikan ayyuka na," in ji Jonathan.