Hukumar NEMA na bincike kan zargin fyade

'Yan gudun hijra a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijra a Najeriya

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya -NEMA, ta kaddamar da bincike kan zargin laifukan da ake aikatawa sansanonin 'yan gudun hijira.

Zargin ya hada da na aikata fyade da fataucin yara da sauran ayyukan cin zarafi a sansanonin 'yan gudun hijirar da rikice-rikicen Boko Haram ya rutsa da su a arewa maso gabashin kasar.

A wani rahoto da cibiyar bincike da aikin jarida ta Najeriya ta fitar, ta ce ta na zargin cewa jami'an da aka wakilta don su kare 'yan gudun hijirar na daga cikin ma su aikata cin zarafin.

Wani babban Jami'i mai kula da ayyukan hukumar ta NEMA a shiyyar arewa maso gabacin kasar, ya shaidawa BBC cewa binciken za a fara shi ta hanyar gudanar da tambayoyi ga 'yan gudun hijira da jami'an hukumar masu gudanar da aiki a sansanonin.

Mutane kimanin miliyan uku da dubu dari biyu ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin kasar.