Wata jami'a a Uganda na bincike kan sakamakon jarabawa

Jami'ar Makerere a kasar Uganda
Image caption Jami'ar Makerere a kasar Uganda

Jami'ar Makerere ta kasar Uganda ta kaddamar da binciken zarge-zargen baiwa daliban da suka fadi jarabawa takardun shaidar digiri na bogi.

Jami'ar ta Makerere dai ita ce mafi girma da kuma dadewa a kasar ta Uganda.

Cikin dalibai dubu goma sha biyun da suka kammala karatu a watan da ya gabata, akalla dari shida ne aka bayyana cewa basu samu sakamako mai kyau ba.

Mataimakin shugaban Jami'ar ya shaidawa BBC cewa ya na zargin akwai wani yunkurin da gan-gan na sauya sakamakon jarrabawa.

Shugaban sashen nazarin aikin jarida na jami'ar (William Tayeebwa) ya ce ya nuna karara yadda wani dalibi da ya fadi jarabawa da kashi 44 bisa dari aka daga shi zuwa kashi 71 bisa dari.