Amurka zata janye dakarunta daga Saliyo

Ma'aikacin asibiti na duba maganin riga kafin cutar Ebola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola ta yi mummunar barna yammacin Afurka.

Jami'an Amurka sun ce kasar na shirin janye wasu daga cikin dakaru dubu sha uku da ta tura yammacin Afurka dan taimakawa a yakin da ake da cutar Ebola, kuma a yau laraba ne ake sa ran shugaba Obama zai sanar da hakan.

Hukumomin Amurkar dai sun yi amanna da cewar a yanzu haka an ciwo kan cutar, haka kuma wani rahoto na 'yan majalisar dokokin Burtaniya ya zargi gwamnatin kasar da tafiyar hawainiya kan batun cutar ta Ebola.

'Yan majalisar sun ce gwamnatin Burtaniya ba ta yi amfani da damar da ta samu ba dan taimakawa yakar cutar a kasar Saliyo, da kuma ta yi hakan da an samu rarar kudade.

A baya dai Burtaniyar ta aike da daruruwan dakarunta da kuma asibitin tafi da gidan ka jirgin ruwa zuwa kasar ta Saliyo.