An bullo da hanyar rufe Facebook na matattu

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Facebook ya dade yana neman hanyoyin taimakawa mutane tunawa da 'yan uwansu da suka mutu

Shafin sada zumunta na Facebook ya bullo da wata hanya ta bai wa mutane damar rufe shafukansu har abada idan sun mutu.

In kuma mutane suna so, za su iya zaban aboki ko dan uwa ya ci gaba da tafiyar da wasu abubuwa a shafukan nasu bayan mutuwar su.

Wadannan sababbin abubuwa da shafin Facebook ya bullo da su, suna daga cikin abubuwan da mutane suka fi nuna bukatarsu daga shafin na Facebook.

Sai dai a yanzu, masu mu'amala da shafin Facebook a Amurka ne kawai zasu iya amfani da sabbin hanyoyin da shafin ya bullo da su.

Mahukuntan Facebook suka ce sababbin tsare tsaren da aka bullo da su zasu sa 'yan uwa da abokan arziki su rika tunawa da wadanda suka mutu.

Idan mutun ya amince wani ya ci gaba da tafiyar da shafinsa na Facebook, za a iya yin rubutu a shafin nasa da karbar sabbin abokai da sauya babban hoton shafin da sauransu bayan ya mutu.

Shafin Facebook ya dade yana neman hanyoyin taimakawa iyalai tunawa da 'yan uwansu, saboda bukatar shiga shafukan mamata da manyan mutane suka yi ta nuna wa.