Kudan Zuma suna jin dadin rayuwa a birane

Kudan Zuma Hakkin mallakar hoto TOBIAS SMITH
Image caption Kudan Zuma

Wani nazari da aka gudanar ya nuna cewar, yankunan maraya a Brittaniya sun zamo wurin zama na Kudan-zuma fiye da kasancewarsu a gonaki.

Kamar yadda binciken ya nuna Filawoyi da ake shukawa a lambuna da gaban gidaje sun zamo wata kafar samun abinci ga Kudan-Zumar a duk tsawon Shekara.

Masana kimiyya sun kididdige Kudajen-zuma da sauran kwari dake samun abinci daga filawoyi a ciki da kewayen wasu daga cikin manyan garuruwa da birane na Brittaniyar.

Suka ce tsirrai da ake shukawa a birane za su iya taka babbar rawa wajen kiwon Kudan-Zuma.

Kudan-zumar da sauran wasu kwarin dake samun abinci daga tsirrai na fuskantar barazana daga bushewar tsirran da magungunan kwari da ake fesawa da kuma cututtuka.

To, amma wani sabon bincike ya nuna cewar Kudajen-Zumar da sauran kwari suna rayuwa a birane da garuruwa kamar yadda suke rayuwa a gonaki da dazuzzuka.

Tawagar masu binciken a karkashin jagorancin Dr Katherine Baldock ta Jami'ar Bristol ta ce akwai bukatar kyautata muhalli a birane wanda girmansa ya kai kashi 7 bisa dari a Brittaniyar don kare Kudan-Zuma daga karewa.

Ta gaya ma sashen labarai na BBC cewar "za a iya kula da yankunan maraya ta yadda kwari masu samun abinci a jikin filawa za su samu abinci. Tace abinda muke bukata shine sanin irin tsirran da kwari suka fi so don shuka su a yankunan maraya.

Ta kara da cewa, a yayinda gonaki suka zamo wurinda ake shukar wasu ko wani nau'i na kayan abinci, lambuna da bakin gidaje sun zamo wasu wurare da ake samun filawoyi a duk tsawon shekara, wanda kuma shine wadannan kwari suke so.

Karin bayani