'Yan gudun hijirar Nigeria na rayuwar kadaici

'Yan gudun hijira a Nigeria. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Miliyoyin mutane ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a arewa maso gabashin Nigeria.

Yayin da ake ci gaba da samun matsalar 'yan gudun hijira sakamakon tarzoma mai nasaba da Boko Haram a Nijeriya da wasu kasashe makotanta, wani lamari dake kara kunno kai shi ne yadda wasu daga cikin 'yan gudun hijirar kan kasance su kadai.

Saboda lokacin da suka baro gida a firgice suke, kowa ya yi nasa wuri inda suka fantsama sassa daban-daban na kasar, Abin anan da ake kira nafsi-nafsi.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun shaidawa BBC cewar ba su san inda 'yan uwan su suke ba, ko a mace ko a raye.

Wata mata da ke sansanin 'yan gudun hijirar ta shaida mana cewar a yanzu haka ta na neman mijinta da 'ya'yan ta har ma da iyayenta ruwa a jallo, saboda a lokacin da suka fantsama kowa ya yi ta kan sa ne.

Haka wani yaro mai shekaru 11 yace ya na rayuwa ne shi kadai ba tare da iyayensa ba, ya kuma ce a halin yanzu babban burinsa shi ne ya yi tozali da iyaye ko kuma wasu daga cikin danginsa.