Cin zarafi ne maganar takardar karatun Buhari - Obasanjo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obasanjo ya ce magana a kan takardun makarantar Buhari abin kunya ne

Tsohon Shugaban Nigeria, Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana cewar cin mutunci a sanya alamar tambaya akan cancatar takardun karatun da ake yi wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Janar Obasanjo ya ce a lokacin da ya shiga aikin soja, wajibi ne mutum ya samu takardar shaidar kamalla karatu ta WASC ko GCE kafin a dauke shi aikin soja.

Ya ce haka kuma abun ya ke lokacin da Janar Buhari ya shiga soja a shekarar 1961.

Janar Obasanjo ya kara da cewa ko da kuma Janar Buhari bashi da wannan takardar, to ai ya halarci makarantar koyan aikin soja wadda ta ke daidai da digiri na farko da kuma kwalejin yaki ta Amurka, wadda ta kammalata ya ke daidai da digiri na biyu.

Janar Obasanjo ya yi bayani ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a birnin Nairobi inda ya kaddamar da littafinsa. Janar din y ace zai yi nazari akan yan takarar biyu ya kuma kada kuru'a a kan mutumin da ya fi kyakkyawan tarihi wajen gudanar da mulki.