Saudiyya: An saki matan da suka bijirewa dokar tuki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Saudiyya ta haramtawa mata yin tuki a baya

Rahotanni daga Saudi Arabia na cewa an saki wasu mata biyu da ake tsare da su fiye da kwanaki saba'in, saboda fafutukar da suka yi na ganin cewa an baiwa mata 'yancin yin tuki.

An kama Loujain Hatlul ne a iyakar Saudi Arabiya da hadaddiyar daular larabawa, a lokacin da take kokarin bijirewa dokar haramta yin tukin motar.

Ita kuma Maysaa al-Amoudi, 'yar jaridar Saudiyyan dake zaune a hadaddiyar daular larabawa--- an tsare tane a wancan lokacin a lokacin da take kokarin taimakawa Loujain.

Masu fafutuka dai sun bayyana damuwarsu game da matan biyu, bayan da aka bada rahotan cewa an tura batun laifin da ake cewa sun aikata zuwa wata kotun yaki da ta'addanci