Duniya ta yi shuru duk da kisan Musulman Amurka

Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption An zargi manyan kafafen watsa labarai da kin jinin musulmai

Manyan kafafen watsa labaran duniya sun yi shuru duk da kisan da aka yi wa wasu musulmai daliban wata makaranta a garin Chapel Hill da ke jihar North Carolina ta Amurka.

An kashe daliban uku ne ranar Talata.

Daliban dai su ne Deah Shaddy Barakat da matarsa, Yusor Mohammad Abu-Salha, mai shekaru 21, da kuma kanwarta, Razan Mohammad Abu-Salha, mai shekaru19.

An kama wani mutum mai suna Craig Stephen Hicks, dan shekaru 46, bisa zargin kisan nasu.

Rahotanni na cewa mutumin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ba shi da addini.

An zargi kafafen watsa labarai da kin jinin musulmai

Da farko dai ba a bai wa labarin muhimmanci ba, har ma 'yan sandan garin suka fitar da sanarwar da ke cewa kisan ya faru ne bayan daliban sun samu rashin jituwa da wanda ake ya kashe su a kan wajen da kowanne zai ajiye motarsa.

Sai dai mahafin Abu-Salha ya musanta wannan zargi, yana mai cewa an yi kisan ne "saboda tsanar da ake yi musu".

Masu fafutika a shafukan intanet sun soki manyan kafafen watsa labaran duniya saboda rashin bai wa batun muhimmanci.

Hakan ne ma ya sa suka kirkiro da wani take mai suna #ChapelHillShooting domin janyo hankalin duniya kan batun, kuma ya zuwa yanzu fiye da mutane 900,000 sun yi amfani da shi.

Hasalima, wannan take shi ne ya fi jan hankulan mutane a Amurka da Burtaniya da Masar da Saudi Arabia da kuma kasashen Gabas ta Tsakiya da dama.

Yawancin wadanda ke amfani da wannan take sun zargi manyan kafafen watsa labarai da cewa ba sa yi wa musulmai adalci, suna masu cewa da a ce musulmi ne ya yi kisan da tuni "an bayyana shi a matsayin dan ta'adda".