'Yan Boko Haram sun kai hari a Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na kokarin kafa daular Musulunci

Kungiyar Boko Haram ta kai harin farko a wani kauye kasar Chadi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane 10.

Wani mazaunin kauyen Ngouboua ya bayyana cewa mayakan Boko Haram din sun zo a cikin kwale-kwale uku, koda yake daga baya sojoji sun fatattake su.

Wata majiya ta ce 'yan Boko Haram kusan 30 ne suka kai hari a kauyen sannan suka bankawa gidaje wuta.

Rikicin Boko Haram ya bazu zuwa kasashen Nigeria da Kamaru da Nijar da kuma Chadi.

Tuni kungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da kafa rundunar mai duke da dakaru fiye da 8,000 domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.