'Ba za a tuhumi Hissene Habre ba'

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata kotu a Senegal ta yanke hukuncin cewa babu isashiyar hujjar yiwa tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre shari'ar aikata laifukan yaki da ganawa jama'a azaba da kuma laifuka akan bil-adama.

Alkalan Kotun-- wacce tarayyar Afirka da kuma Senegal suka kafa, sun yi hira da shaidu fiye da 2000 a shekaru biyun da suka gabata.

Ana zargin Mr Hissene Habre da kashe dubun- dubatar rayuka da suka danganci siyasa a lokacin mulkinsa na shekaru takwas, wanda ya kare a shekarar 1990 a lokacin da aka hanbarar da shi.