Kungiyar IS ta yi garkuwa da Kibdawa 21

Hakkin mallakar hoto c
Image caption Kungiyar IS ta kashe wasu mutanen da ta yi garkuwa da su a baya

Shugaban Masar, Abdul Fattah al-Sisi ya yi tayin kwashe 'yan kasarsa daga kasar Libya, bayan masu da'awar kafa daular Musulunci sun wallafa wasu hotuna na kama kiristoci Kibdawa 21.

Hotunan da aka wallafa a shafin intanet sun nuna Kibdawan sanye da riguna masu hade da wando ruwan goro.

Yayin da wasu mutane da suka rufe fuskokinsu da ke sanye da bakaken kaya suka sa Kibdawan maci a bakin teku.

Shafin intanet da ake dangantawa da kungiyar IS ta bayyana mutanen da cewa mayakan kiristoci Kibdawa ne.

Kuma sun kama su ne a matsayin ramuwar gayya na sace matan Musulmi tare da azabtar da su da Cocin Kibdawan ke yi a Masar.

Ma'aikatan harkokin wajen Masar ta jaddada kiran da take yi wa 'yan kasar da kada su je kasar Libya.