Rikici ya sake barkewa a Ukraine

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabon rikicin ya zo ne kwana daya kafin fara aiki da sabuwar yarjejeniya

An kara samun barkewar rikici a Ukraine duk kuwa da sabuwar yarjejeniyar da aka kulla da ake saran zata soma aiki a ranar Asabar da tsakar dare

An ji karar harbe harbe da safiyar Juma'ar nan a garin Donesk inda 'yan tawaye suke da iko, sannan an ji karar harbe harbe a Luhansk a ranar Alhamis

Shugabannin Kasashen Rasha da Ukraine sun amince da kawo karshen fadan tare da shugabannin faransa da Jamus

Shugabannin kasashen Turai sun ce za su kakaba wa Rasha karin takunkumi idan ta ki mutunta sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma agame da gabashin Ukraine.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce tuni Tarayyar Turan ta fara tanadin karin takunkumin.

A ranar Asabar mai zuwa ne aka ce yarjejeniyar tsagita wutar za ta fara aiki.