Gombe: An shiga yini na biyu na dokar hana fita

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption yini na biyu bayan kai hari a Gombe

An shiga yini na biyu da sanya dokar hana fita ba dare ba rana a garin Gomben arewacin Nigeria bayan hare haren 'yan Boko Haram a ranar Asabar.

Wasu mazauna garin na Gombe sun bayyana cewa dokar ta hana su yiwa mamata jana'iza.

Rahotanni sun ce an tsaurara tsaro a garin Gomben da kuma kewayensa

Mazaunan wasu yankunan Jihar Gombe sun ce 'yan Boko Haram din sun rarraba wasu takardu, suna yi wa jama'a kashedin cewa kada su fita su yi zabe a lokacin da suka kai harin.

Karin bayani