Ukraine: Rasha ta ba 'yan tawaye makamai

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rahotanni sun ce an tsallaka iyakar Rasha da manyan makamai

Amurka ta ce ta damu matuka a game rahotannin da ke cewa Rasha na ci gaba da taimakawa 'yan tawaye da makamai a gabashin Ukraine, inda fada ya sake kazancewa duk da sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Mrs Jen Psaki ta ce Rasha ta sabawa manufar yarjejeniyar da ta ci gaba da turawa 'yan tawaye tankokin yaki.

Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ya ce wani makamin roka da 'yan tawayen suka harba Artemivsk wanda ya kashe fararen hula 3, ya sa yarjejeniyar tana kasa tana dabo.

Kakakin rundunar sojin Ukraine Andriy Lysenko ya ce sojoji 11 ne suka mutu a bata kashin a Donestsk da Luhansk, sannan wasu 40 suka samu raunuka.