Ebola: Za a sake bude makarantu a Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters

A yau ne ake saran sake bude makarantu a Liberia, watanni bakwai bayan an rufe su, a kokarin da akai na takaita yaduwar cutar Ebola

Yawan masu fama da cutar a kasar ya ragu sosai.

Ma'aikatar ilmi ta Liberia tace za'a takaita yawan daliban dake cikin aji zuwa mutum 50, domin samu saukin yaduwar duk wata cuta.

A watan da ya gabata ne ita ma kasar Guinea ta sake bude makarantun ta.

Saliyo kuma na shirin yin hakan a karshen watan gobe