An kara yawan jami'an tsaro a Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An jibge sojoji a Gombe da kewaye

Rahotanni daga jihar Gombe a arewa maso gabashin Nijeriya na cewa an tura Karin dakarun tsaro a jihar.

An ce an jibge jami'an tsaron masu yawa akan titunan cikin damara, a birnin na Gombe da kewaye.

Hakan ya biyo bayan hare-haren da mayakan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai wa birnin da ma wasu garuruwa a cikin jihar, ranar Asabar.

Har yanzu dai dokar hana fita ba-dare- ba-rana na ci gaba da aiki, inda kuma jami'an tsaron ke korar duk wanda ya yi yunkurin fita waje.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan rundunar sojin kasar taci alwashin kakkabe 'yan kungiyar Boko Haram daga garuruwan da suka kama.