Sojin Nigeria sun shiga dajin Sambisa — Sambo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Nigeria na fuskantar sukar kasa kawo karshen matsalar Boko Haram

Mataimakin Shugaban Nigeria, Alhaji Muhammad Namadi Sambo, ya bayyana cewa sojojin Nigeria sun kaddamar da farmaki a kan sansonin 'yan kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa.

Namadi Sambo ya ce wannan wani bangare ne na yunkurin da ake yi na tabbatar da samun kwanciyar hankali har a gudanar da zabe ranar 28 ga watan Maris.

Dangane da yiwuwar murkushe 'yan Boko Haram cikin makonni shida kuwa, Alhaji Namadi Sabo ya ce "Ba an ce wai za a wayi gari ba ne a cikin makonni shida a kori duk 'yan Boko Haram, abin da ake cewa shi ne za a tabbatar da cewa an kawo yanayi a kasar nan da zai kyale yanda za a samu a yi zabe a ko'ina a kasar nan".

Hukumar zaben Nigeria dai ta jinkirta zaben kasa baki- daya ne bisa abin da ta ce bukata ce da hukumomin tsaron kasar suka gabatar mata, ta neman makwanni shida domin tunkarar 'yan kungiyar Boko Haram.