'Yan Nijar sun koka da kama sun da ake a Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Image caption An zargi wasu 'yan Nijar da mallakar katinan zabe a Najeriya

Kungiyar 'yan Nijar mazauna kasashen waje reshen Najeriya ta koka game da kamen da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta yi wa 'ya'yanta saboda zargin sun mallaki katinan zabe na din- din- din.

A kwanakin baya ne hukumar ta bayyana cewa ta cafke kusan mutane 200 'yan kasashen waje da katunan na din-din-din, wanda hukumar ta ce hakan ya saba ka'idar zaman su a Nigeriar.

Mafiyawan wadanda aka kama 'yan Niger ne, akwai kuma 'yan kasar Ghana.

Shugaban Kungiyar 'yan Nijar a Nigeria ya shaidawa BBC cewa kamata ya yi a nuna musu wadannan mutane da aka kama da sunan 'yan Nijar ne, domin su tabbatar da inda suka fito

Alhaji Abubakar Khalidu ya kara da cewa kafin a tasa keyar 'yan kasar su , kamata ya yi a fara shaidawa jakadan Niger din a Nigeria