Rikici tsakanin Obasanjo da Goodluck ya yi zafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An jima ana musayar kalamai marasa dadi tsakanin Obasanjo da Jonathan

A Najeriya, takaddama na kara yin zafi tsakanin bangaren shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan da kuma tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo.

Cif Olusegun Obasanjon dai ya yi zargin cewa shugaba Jonathan ya dage babban zaben kasar ne domin ya samu hanyar tankwara zaben, ko ci gaba da mulkin kasar ko ta halin kaka.

Sai dai Kwamitin yakin neman zaben shugaban Jonathan ya musanta wannan zargi, yana cewa ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata irin wannan maganar ta fito daga bakin dattijo kamar Cif Obasanjo ba.

Shima kakakin shugaba Jonathan ya musanta zargin, yana sukar Cif Obasanjo da cewar yana kulla makarkashiya ne domin a nada shi shugaban Gwamnatin rikon-kwarya a Najeriya.