Kamfanin kera motoci na Tesla ya samu faduwa

Kamfanin Tesla ya samu faduwar dala miliyan 108

Asalin hoton, TESLA MOTORS

Bayanan hoto,

Kamfanin Tesla ya samu faduwar dala miliyan 108

Kamfanin Tesla mai kera kananan motoci ya sanar da faduwar da ya sake samu ta dala miliyan 108, in aka kwatanta da faduwar dala miliyan 16 da ya samu a irin wannan lokaci a bara.

A watan Janairu, shugaban kamfanin Elon Musk ya yi gargadin cewa cinikin motocinsu a China ya ragu sosai.

Hannayen jarin kamfanin na Tesla sun fadi da kashi 3 cikin dari.

Bugu da kari, kamfanin ya ce tsaikon da ake samu na kera motoci ya haddasa karancin motocin da ake kai wa kasuwannin duniya, kasa da yadda aka yi tsammani.

Kamfanin ya ce ya kera motoci 11,627, amma 9834 ne kadai aka kai su kasuwannin duniya a lokacin da aka samu faduwar.

Kamfanin na Tesla ya ce ya yi shirin kai motoci 55,000 samfarin Model S da X a cikin wannan shekarar zuwa kasuwannin duniya, adaddin da ya haura wadanda ya kai a cikin shekarar 2014 da kashi 70 cikin dari.