An bukaci MDD ta yi amfani da soji a Yemen

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan tawayen Houthis sun kifar da gwamnatin Abdlrabbus Mansour Hadi cikin watan jiya

Ministocin harkokin wajen kasashen larabawa na yankin Tekun Fasha sun yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya ba da umurnin amfani da karfin soji a Yemen domin magance matsalar siyasa a kasar.

A cikin watan jiya ne 'yan tawayen Houthis masu akidar Shi'a suka hambarar da gwamnatin kasar a Sana'a bayan sun shafe watanni suna sa'in sa da shugaba Abdulrabbuh Mansour Hadi.

Kasashen da ke makwaftaka da Yemen su ka ce abinda ya faru a kasar, juyin mulki ne, saboda haka yakamata Majalisar Dinkin Duniya data sa baki.

Mambobin kwamitin sulhu na Majalisar sun fara nazari akan wani daftarin kuduri, da zai bukaci 'yan tawayen Houthin su gaggauta janyewa daga gine ginen gwamnati, sannan su saki shugaba Mansour Hadi da ministocinsa daga kullen talala.

Kasashe 9 da suka hada da Amurka da Saudiyya sun rufe ofisoshin jakadancin su a kasar saboda fargabar 'yan tawayen Houthis za su mamaye karin yankuna, abinda zai kara wa kungiyar Al'qaeda a kasar karfi.