Obasanjo ya fita daga jam'iyyar PDP

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obasanjo ya soki Mr Jonathan bisa rashin iya gudanar da mulki

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya fita daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Da yake jawabin ficewarsa daga jam'iyyar, Cif Obasanjo ya bukaci shugaban mazabarsa na jam'iyyarta PDP, watau mazabar 11 Ita-Eko, Sumonu Oladunjoye, ya yaga katinsa na kasancewarsa dan jam'iyyar.

Nan take Sumonu Oladunjoye ya bi umarnin Cif Obasanjo.

Obasanjo, wanda ya yi wa 'yan jarida jawabi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, ya kara da cewa ba zai shiga wata jam'iyyar ba, yana mai cewa ya gwammace ya ci gaba da kasancewa "uban kasa".

Obasajo dai ya soki shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki, yana mai cewa Mr Jonathan na so ya sake cin zaben kasar ko ana so ko ba a so idan ba haka ba kuwa zai jefa kasar cikin rikici.

Cif Obasanjo ya zama shugaban Najeriya sau biyu, kuma shi ne ya zabi shugaba Jonathan domin zama mataimakin marigayi shugaba Umaru 'Yar Adua.