2015:Soyinka ya caccaki Jonathan da Buhari

Image caption Soyinka bai da gwani a cikin 'yan takara

Shahararren marubucin nan dan Nigeria, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kakkausar suka a kan manyan 'yan takarar shugabancin kasar a zabukan watan gobe.

A hirarsa da Will Ross na sashin turanci, Soyinka ya ce akwai 'yan takarar da suka fi dacewa fiye da Goodluck Jonathan da kuma Muhammadu Buhari, yan mai bayyanasu a matsayin 'yan takara "masu matsaloli".

Soyinka ya ce, "Masu zabe na cikin halin tsaka-mai-wuya a kan wadannan 'yan takarar saboda duk suna da nasu matsalolin."

Ya kara da cewar saboda irin tarin matsalolin da Nigeria ke ciki taswirar kasar ba za ta kasance iri daya ba nan da shekaru goma masu zuwa.

A kan batun sace 'yan matan Chibok kuwa, Soyinka ya ce, "Abin da ya faru alama ce ta kasawar shugabanci kuma ta'azarar rikicin Boko Haram ya rataya ne a kan shugaba Jonathan."

A kan Buhari kuwa, Furofesa Soyinka ya ce, "Buhari da Janar Idiagbon sun kasance sojoji masu kama-karya."

A ranar 14 ga watan Fabarairu ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasa amma sai aka dage zuwa 28 ga watan Maris bisa dalilan tsaro, amma mutane da dama na zargin cewa dalilan siyasa ne suka janyo aka jinkirta zaben.