Fyade: Mata a Turkiya na zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana cin zarafin mata sosai a duniya

Mata a kasar Turkiya sun fara wani kamfe a shafukan zumunta na zamani, bayan sun gudanar da zanga-zanga don yin Allah-wadai da cin zarafin da su ke fuskanta.

Matan sun wallafa hotunansu sanye da bakaken kaya don jimamin mutuwar wata matashiya wacce aka samu gawarta a kone a ranar Juma'a, bayan da ta ki yarda wani matukin motar bas ya yi mata fyade.

Matan na Turkiya suna kuma ba da labaran irin abubuwan da suka fuskanta na barazanar cin zarafi da tashin hankali a shafukan zumunta na zamani.

Masu fafutuka sun ce kusan mata 300 ne mazajen kasar su ka kashe a bara.

Aysenur Islam, wacce ita ce minista mace daya tal a kasar, ta bayar da shawara cewa a dinga yanke hukuncin kisa kan irin wadannan laifuka.