'Yancin kananan hukumomi ya samu cikas

TASWIRAR NIGERIA Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption TASWIRAR NIGERIA

A Najeriya, kokarin da majalisar dokokin Najeriya ke yi na kafa dokar bai wa majalisun kananan hukumomin kasar 'yancin-cin-gashin-kai bai yi nasara ba a karo na biyu.

Wannan dai ya fito fili ne a yau,Talata, lokacin da majalisar wakillan Najeriya ta karbi rahoton kuri'un da majalisun dokokin jihohin kasar 36 suka jefa kan yin gyaran-fuska ga kundin tsarin mulkin kasar wanda ya hada har da batun na cin-gashin-kan kananan hukumomin.

Majalisun dokokin jihohi 20 daga cikin 36 ne suka amince da kwace ikon kananan hukumomin daga hannun gwamnonin jihohi abin ya kasa kai kashi biyu bisa uku da ake bukata wato jihohi 24 kenan.