Mun kashe 'yan Boko Haram 80 — Kamaru

Sojin Kamaru. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen da ke makwaftaka da Nigeria sun lashi takobin murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin Kamaru ta ce sojojinta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 80, wadanda suka tsallaka iyakar kasar daga Nigeria tare da kai hari a wani sansanin sojin kasar.

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar, Canal Didier Badjeck, ya ce an kuma kashe sojin Kamaru biyar a yayin fafatawar da aka yi da 'yan Boko Haram din.

Kasashen Kamaru da Jamhuriyar Nijar da ke fuskantar hare-haren 'yan kungiyar, sun ce kawo yanzu sun cafke daruruwan mutane da ake zargin su na da alaka da Boko Haram.

Za mu murkuseh Boko Haram

A bangare guda kuma, shugabannin kasashe shida na yammacin Afirka na wata tattaunawa a babban birnin kasar Kamaru wato Yaounde, domin gano hanyar da za su hada karfi da karfe domin kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram.

Hamid Alami shi ne Sakatare Janar na kungiyar, ya kuma ce wannan abu ne mai cike da tarihi, yana mai cewa ana bukatar daukar matakin gaggawa game da munanan ayyukan da masu tayar da kayar baya na Boko Haram ke yi saboda barazanar da suke yi ga zaman lafiyar Afirka.