An yi zanga-zanga a Accra da Lagos kan wutar lantarki

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Rashin samun isasshiyar wutar lantarki dai ya sa kamfanoni da dama sun daina aiki a Najeriya.

'Yan babbar jam'iyyar adawa a Ghana, NPP sun yi zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da yawan dauke wutar lantarki a kasar.

Masu zanga-zangar, wacce dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Nana Akuffo Addo ya jagoranta, sun koka kan yadda gwamnati ta gaza shawo kan matsalar duk da makudan kudin da ake kashe wa kan batun.

Sun yi kira ga gwamnati ta inganta lamarin domin 'yan kasar su ci gaba da gudanar da harkokinsu na tattalin arziki da kuma walwala.

Kazalika, wasu mazauna birnin Lagos na Najeriya sun gudanar da zanga zangar lumana, zuwa daya daga babbar tashar samar da wutar lantarki ta Ijora a Lagos.

Mazauna gidajen Village games da wasu da suka bi sahunsu sun koka a kan karancin wutar lantarki da kuma karbar kudin wuta duk da cewa babu ita.

Rashin samun isasshiyar wutar lantarki dai ya sa kamfanoni da dama sun daina aiki a Najeriya.