Ku fito ku karbi katin zabe —Sarkin Kano

Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Susuni na biyu Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jihar Kano na daga cikin jihohin arewacin Nigeria da suka sha fuskantar hare-haren kungiyar Boko Haram.

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya yi kira ga jama'ar jihar da ba su karbi katinansu na zabe ba, su je su karba kafin wa'adin bayar da katin ya wuce.

Sarkin ya yi wannan kira ne a fadar sa yayin wani taro na manema labarai.

Sarkin na Kano dai ya ce matukar jama'a ba su karbi katinansu ba, to yawan jama'ar jihar zai zama ba shi da amfani.

Jihar Kano dai na daga jihohin da hukumar zabe tace mutane da dama ba su karbi katinan su na zabe ba.

Wasu bayanai dai da hukumar zaben Nigeria ta fitar a ranar Talata sun nuna cewa kashi 76 ne na masu kada kuri'a suka karbi na katunan zabe a duk fadin Nigeria, kuma jihar Zamfara ke kan gaba da yawan wadanda suka karbi katunansu.

Kazalika jihar Kano -- wacce ke da masu kada kuri'a kusan miliyan biyar-- ta karbi kashi 70 cikin 100 na katinan zabenta.