Boko Haram: Niger ta yi gangamin goyon bayan soji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dokokin Nijar ta amince a tura dakarun kasar Najeriya da Kamaru da kuma Chadi

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun shirya wata zanga-zangar lumana a fadin kasar, a wani mataki na nuna goyon baya ga jami’an tsaro a yakin da suke yi da Boko Haram.

Wadanda suka halarci zanga-zangar sun hada da shugaban kasar, Alhaji Mahamadu Issoufuo, wanda ya jaddada aniyarsa ta yakar kungiyar ta boko haram.

Zanga-zanga ta biyo-bayan wasu jerin hare-hare da kungiyar ta Boko Haram ta kai a yankin jahar Diffa, mai makwabtaka da jahohin Borno da Yobe a Najeriya.

Hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar jami’an tsaro da dama da daruruwan 'yan kungiyar ta Boko-Haram.

Haka kuma dukkan mazauna garin Diffa ne suka tsere zuwa Damagaram da wasu jihohi na kasar, domin gujewa hare-haren Boko Haram.

Sai dai 'yan adawa sun kauracewa zanga-zangar ta Nijar, suna cewa siyasa ce kawai.