'Majalisa za ta bijirewa kafa gwamnatin riko'

Hakkin mallakar hoto aliyu

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bijirewa duk wani yunkuri na kafa gwamnatin rikon-kwarya a kasar.

Da yake jawabin bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata, Shugaban Majalisar, Sanata David Mark, ya umarci hukumar zaben kasar da ta ci gaba da shirye-Shiryen yin zabe.

Mr. Mark ya ce majalisar za ta tabbatar da cewa an rantsar da sabuwar gwamnati da aka zaba ta hanyar zabe mai sahihanci a ranar 29 ga watan Mayu.

Hukumar zaben dai ta sanya ranakun 28 ga watan Maris da kuma ranar 11 ga watan Afrilu na wannan shekara.

Ministan shari'a na kasar Bello Adoke ya ce babu batun gwamnatin rikon kwarya a kundin tsarin mulkin Najeriyar.