Mun ji takaicin ficewar Obasanjo — PDP

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obasanjo ya ce tura ta kai bango

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta ce ta ji takaicin ficewar tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo daga cikin jam'iyyar.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar PDP, Oliseh Metu ya fitar, jam'iyyar ta ce duk da kamun kafar da aka yi ta yi domin rarrashin Obasanjo amma kuma yaki ji har ta kai ga a yanzu ya bar PDP.

Cif Obasanjo ya sanarda ficewarsa daga PDP ne a ranar Litinin a wani taro da ya kira a Abeokuta babban birnin jihar Ogun, inda ya umurci shugaban PDP a mazabarsa ya keta katinsa na shaidar zama dan PDP.

Obasanjo ya jagoranci Nigeria na tsawon shekaru takwas a karkashin inuwar jam'iyyar PDP sannan kuma ya shugabancin kwamitin amintattunta na wasu shekaru bayan saukarsa daga kujerar mulkin Nigeria.

Sanarwar ta PDP ta kuma bukaci 'ya'yanta su mayar da hankali a wajen yakin neman zabe domin samun nasara a zabukan da ke tafe a watan Maris da kuma Afrilu.

Matakin Obasanjo na zuwa ne bayan shafe lokaci mai tsawo yana caccakar salon mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.