An kai hari a taron APC a jihar Rivers

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Rotimi Amaechi na Rivers

An kai hari a taron yakin neman zaben da jami'yyar APC ke yi a Okirika na jihar Rivers a kudancin Nigeria inda aka yi ta harbe-harben bindiga a filin taron.

Reshen jihar Rivers na jam'iyyar APC ne ke gudanar da taron a filin wata makarantar sakandare da ke Okirika, wato mahaifar uwargidan shugaban Najeriya, Patience Jonathan.

An dai ji karar fashewar wasu abubuwa a wasu wurare kusa da inda ake yin taron, amma kawo yanzu babu cikakken bayani a kan wadanda suka rasa rayukunsu ko kuma jikkata.

Kawo yanzu babu wata sanarwa daga mahukunta ko jami'an tsaro dangane da wannan lamari.

Bangaren jam'iyyar adawa ta APC da jam'iyyar PDP sun dade suna takun-saka da juna tare da zargin kai hare-hare.