Za a dakatar da bude wuta a Syria

Shugaba Basharul Assad na Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dai kwashe sama da shekaru 3 ana gwabza fada tsakanin 'yan tawaye da sojojin kasar Syria.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Staffan de Mistura, ya shaidawa kwamitin tsaro na majalisar cewa Damscuss a shirye ta ke ta dakatar da luguden wutar da ta ke a birnin Aleppo har na tsahon makwanni 6 a wani bangare na shirin MDD na dakatar da wuta.

Mr de Mistura yace gwamnatin Syria yace wannanalwashi da ta yi ya dan bada kwarin gwiwa ko da yake ba asan lokacin da dakatarwar za ta fara aiki ba.

Sai dai yace gwamnatin Syria ta yi msa sa nuni da cewar a shirye take da dakatar da dukkan wasu hare-hare ta sama da take kaiwa a yankin, da kuma sauran hare-hare ta kasa da manyan makaman atilari na tsahon makwanni 6 a dukkan birnin Aleppo.

Amma kungiyar 'yan adawa ta Syrian National Council ta ce za su amince da wannan kira da gwamnatin kasar ta yi ne kawai idan sun ga hakan a aikace ba wai ta fatar baki ba.

Dakarun sojin Syria dai na ci gaba da luguden wuta ya yin da suke kokarin katse hanyar da 'yan tawaye ke amfani da ita abirnin na Aleppo.

Rahotanni sun bayyana cewa fiye da sojoji dari da 'yan tawaye aka kashe a jiya talata.