Ana kokarin samar da sabon maganin Polio

Malaman Polio
Image caption Malaman Polio

Tawagar wasu kwararrun likitoci ta duniya na kokarin kirkirar wani maganin riga-kafi guda daya da za a yi amfani da shi wajen kawar da cutar shan-inna.

Ana gab da kawar da cutar, 'yan daruruwa ne ake samu a kowacce shekara.

Fatar ita ce sabuwar hanyar za ta iya kawar da wasu matsaloli da ake cin karo da su a maganin da ake amfani da shi a yanzu, don haka za ta iya taimakawa wajen kawar da cutar shan-innar baki-daya.

Hukumar lafiya ta duniya WHO da Gidauniyar Bill da Melinda Gates za su ba da tallafin kudi dala 673,000 domin wannan aiki.

An bayar da sanarwar ne a wajen taron shekara-shekara ne na Kungiyar kawo cigaban kimiyya ta Amurka a San Jose dake California.

Masu bincike a Amurka da Brittaniya za su shiga a tawagar masu kokarin kirkiro wannan maganin.

A Brittaniya, wannan aiki zan janyo ma'aikata daga Leeds da Oxford da Reading da kuma Diamond Synchrotron.

Ana dai gab da ciwo kan cutar ta Shan-inna.

Wurinda a da ake samun mutane daruruwan dubbai dake kamuwa da cutar a duniya, a bara an ba da rahoton mutane 350 ne kawai da suka kamu da cutar, kuma yawancinsu a kasar Pakistan ne.

To, sai dai kuma yunkurin na karshe na haduwa da cikas. Daya daga cikin dalilan sun ta'allaka ne a kan dalilai na maganin da ake amfani da shi na digawa wanda sinadarin dake cikinsa na cutar ne mai rauni kamar irin tasirin da ya kan yi wajen aiki na kariya da warkar da masu dauke da kwayoyin vutar.

A jikin wasu 'yan tsiraru, wannan zai sa kwayar cutar ta taso ta yadu ga wasu wadanda ba a yi ma riga-kafi ba.

To amma idan kwayar cutar ba ta da kwayar halitta mai yaduwa, cutar ba za ta yadu ba, kuma hukumar lafiya ta duniya da Gidauniyar Bill da Melinda za ta dauki nauyin masana kimiyya da za su maganin da zai maye gurnin wanda ake amfani da shi a yanzu.

Karin bayani