Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 300

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dakarun Nigeria na yaki tare da hadin gwiwar wasu kasashe domin murkushe ayyukan Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta yi ikirarin kashe 'yan kungiyar Boko Haram fiye da 300 a wasu hare-hare ta sama da kasa da ta kai musu.

Rundunar wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta Manjo Janar Chris Olukolade ya sanya wa hannu, ta ce ta kama 'yan kungiyar ta Boko Haram da dama da motoci da makamansu.

Chris Olukolade ya kara da cewa soji sun kwato garuruwa da dama da suka hada da: Monguno, Gabchari, Abba Jabari, Zuntur, Gajigana, Gajiram, Damakar, Kumaliwa, Bosso Wanti, Jeram da kuma Kabrisungul.

A cewarsa, an kama motocin yaki masu sulke iri biyar, da bindigar harbo jiragen sama, da kwanson bam 50 da manyan bindigogi guda biyar.

Rundunar sojin ta ce a lokacin ba-ta kashin, an kashe sojoji biyu tare da raunata wasu 10.

Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane fiye da 13,000 cikin shekaru shida a Nigeria.