CBN ya sayar da dala sama da farashin hukuma

Image caption Masana sun yi hasashen faduwar darajar naira zai janyo yaduwar talauci da rashin aikin yi a Najeriya

Rahotanni sun ce babban bankin Najeriya, CBN, a karo na uku ya sayar da dalar Amurka a kan farashin da ya haura abin da ya kayyade bayan ya rage darajar kudin a watan Nuwambar bara.

Bayanai sun ambato masu hada-hadar kudade na cewa babban bankin ya sayar da ko wacce dalar Amurka a kan naira 198, sabanin farashin da ya kayyade na tsakanin naira 160 zuwa naira 176.

Sai dai kuma duk haka, darajar naira na ci gaba da faduwa, inda a ranar Talata aka sayar da dala a kan sama da naira 200.

Wasu masana tattalain arziki na ganin "Kowa ya sayi rariya ya san za ta yi zuba."

Inda suka ce lokacin da aka rage darajar naira ba da ce ba, ganin tatalin arzikin Najeriyar ya hadu da rigingimun siyasa kuma ba a kai ga samar da kayyakin da kasar ke sayarwa a waje ba.

Masanan sun kuma danganta tangal-tangal da naira ke yi da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya da kuma hauhawar farashin kayayyaki a kasar.