An ceto 'yan Afrika 4000 a gabar tekun Italiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daruruwan 'yan Afrika ne ke mutuwa a tekun Bahar rum kafin su isa Italiya duk shekara

Hukumar 'yan ci-rani ta duniya ta ce a cikin kwanaki biyar da suka wuce, an ceto 'yan ci-rani 4,000 da ke kokarin ketara Bahar Rum daga arewacin Afrika.

Shugaban hukumar ya jinjinawa jami'an tsaron bakin teku da sojojin ruwa na Italiya wajen ceton 'yan ci-ranin.

Yayin da Fafaroma Francis ya bayyana cewa jami'an sun ceto mutanen da ke cikin wani hali.

Ministan harkokin wajen Italiya ya ce yawan 'yan ci-ranin da suka isa kasar a farkon makonni shida na farkon wannan shekara, a yanzu ya rubanya da kashi 60 cikin dari idan aka kwatanta da bara.

Da dama daga cikin 'yan ci-ranin dai na fitowa ne daga kasashen Afrika na Kudu da Sahara, inda suke bi ta Libya domin isa nahiyar Turai.