Jega ya bayyana a gaban Majalisar Dattawan Nigeria

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Dage babban zaben Najeriya ya janyo cece kuce a ciki da wajen kasar

Shugaban hukumar zaben Nigeria, farfesa Attahiru Jega ya bayyana a gaban majalisar dattawan kasar inda ya yi jawabi game da shirye-shiryen babban zabe na kasar.

A jawabin nasa, Jega ya ce kundin tsarin mulki da kuma dokar zabe sun ba hukumar ikon amfani da na'urar tantance katin zabe, inda ya jaddada cewa INEC za ta yi amfani da na'urar ce wajen tantance masu kada kuri'a ba wajen kada kuri'a ba.

Haka kuma ya kara da cewa an dage babban zaben kamar yadda aka shirya a baya ne a bisa shawarwarin da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro da hafsoshin sojin kasar suka bayar.

Jami'an hukumar ta INEC sun gwada yadda na'urar tantance masu zabe ke aiki ta hanyar gwada katunan dundundun na wasu 'yan majalisar a zauren majalisar.

'Yan majalisar dai na yi wa shugaban hukumar zaben tambayoyi game da na'urar tantance katin masu zabe da kuma yadda hukumar ta shirya yin zabe a karshen watan gobe da watan Afrilu masu zuwa.

Yayin da shi kuma farfesa Jega ke amsa tambayoyin nasu daya-bayan daya.