Boko Haram ta fitar da hotunan harin Gombe

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Mayakan Boko Haram a cikin Gombe

Kungiyar Boko Haram ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Twitter wadanda ta yi ikrarin mayakanta ne a lokacin da suke kai hari a garin Gombe a makon daya gabata.

Kungiyar ta nuna yadda mayakanta suka shiga garin Gombe dauke da manyan makamai a kan tituna.

Ta wannan shafi ne dai shima shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fitar da bidiyonsa na baya bayan nan

Hotunan sun nuna 'yan Boko Haram su kadai a kan tituna kusa da wani babban ginin gwamnati a cikin birnin, sai dai babu wasu alamu na jami'an tsaro.

Haka kuma a shafin na twitter kungiyar Boko Haram ta nuna wani bidiyo da ta kira ''dandano'' inda mayakanta ke barin wuta sannan kuma ga wasu mutane da kayan sojin Nigeria a kwance a kasa sun mutu.

A cikin wannan bidiyon da bai kai twason minti biyu ba, kungiyar ta nuna yadda mayakanta ke sarrafa manyan makamai da kuma motoci masu sulke.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a yayinda mutane fiye da miliyan uku suka rasa muhallansu.