Sojin Chadi sun kwato Dikwa daga Boko Haram

Hakkin mallakar hoto none
Image caption A kwanakin baya sojin na Chadi suka kwato garin Gamboru daga hannun 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Chadi ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kwato garin Dikwa da ke jihar Borno ta Najeriya.

Rundunar ta ce ta kwato garin ne ranar Talata da almuru bayan ta fafata da 'yan kungiyar ta Boko Haram da ke rike da shi.

Wani mai magana da yawun sojin Chadin ya ce sun kashe 'yan Boko Haram 117 a fafatawar, yayinda sojin Chadi biyu suka rasa rayukansu.

Garin dai yana da nisan kilomita 50 daga garin Gamboru.

Rahotanni sun ce sojin na Cahdi sun kai harin kan 'yan boko Haram din ne daga garin Gamboru, wanda a kwanakin baya suka kama.

Kasashen yankin Chadi da Benin sun hada gwiwa domin yaki da kungiyar ta Boko Haram, wacce ke fadada hare-harenta.