Balotelli ya nuna rashin 'ladabi' - Gerrard

Image caption Balotelli ya karbi kwallo daga hannun Henderson

Steven Gerrard ya zargi Mario Balotelli da nuna rashin "biyayya" saboda buga fenariti a wasansu da Besiktas.

Balotelli ya buga fenariti din a raga bayan da ya yi jayayya tsakaninsa da kyaftin din kungiyar Jordan Henderson da kuma Daniel Sturridge wadanda suka nuna kwadayin buga fenariti din.

Gerrard ya ce "Henderson ne kyaftin kuma Balotelli ya nuna masa rashin ladabi."

A cewar Gerrard bai kamata Balotelli ya karbi kwallon ya buga ba.

Liverpool ta samu galaba a wasan da ci daya mai ban haushi a wasan na gasar Europa a filin Anfield tsakaninta da Besiktas.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers bai ce komai ba kan batun.